26 Mayu 2021 - 11:09
​Syria: A Yau Ne Ake Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa

Al’ummar kasar Syria na ci gaba da kada kuri’unsu a kwatunan zabe a zaben shugaban kasa a sassan kasar.

ABNA24 : Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, tun da safiyar yau ne aka bude rumfunan zabe a fadin kasar Syria domin kada kuri’a a zaben shugaban kasa, inda jama’a suke ci gaba da yin dafifi a mazabu domin kada kuri’unsu.

Tun a makon da ya gabata ne dai aka fara gudanar da zaben ga ‘yan Syria mazauna kasashen ketare, duk kuwa da cewa wasu daga cikin kasashen turai sun hana ‘yan kasar Syria mazauna kasashensu gudanar da zaben, amma wasu daga cikin kasashen turan da ma sauran kasashen duniya da dama hard a na larabawa, sun bar ‘yan kasar Syria mazauna kasashensu sun kada kuri’unsu.

Zaben dai yana gudana lami lafiya ba tare da wani yamutsi ko tashin hankali ba, kuma ‘yan takara uku ne suke fafatawa da juna, da suka hada da Abdullah Salum Abdulla, Da Bashar Hafez Assad, da kuma jagoran ‘yan adawa na cikin kasar ta Syria Mahmud ahmad Mar’i.

Kasar Syria dai ta yi fama da tashin hankali a shekarun baya, a lokacin da wasu kasashen turai da wasu larabawa da ba su dasawa da ita suka shirya kifar da gwamnatin kasar ta hanyar yin amfani da ‘yan ta’addan daga ko’ina cikin fadin duniya.

Amma sakamakon tsayin dakan da al’ummar kasar suka yi, da kuma mara baya da kasar ta samu daga manyan kawayenta Iran da Rasha, hakan yasa shirin rusa kasar ta Syria bai yi nasara ba, inda daga karshe dai Syria ta yi nasara wajen murkushe ‘yan ta’adda wadanda da dama daga cikinsu an halaka su, wasu kuma sun koma kasashen da suka fito.

342/